ABNA24 : Grossi ya sami tarbar kakakin hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi a filin saukar jiragen sama na Imam Khumaini na kasa da kasa.
Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaban hukumar makamashin Nukiliyar Grossi ya kawo Iran, tun bayan hawansa kan mukaminsa a ranar 3 ga watan Disamba na 2019.
A cikin rahotanni 17 da hukumar ta fitar, ta tabbatar da cewa Iran tana bayar da hadin kai ga hukumar ta kasa da kasa.
Daga cikin wadanda shugaban hukumar ta kasa da kasa zai gana da su a yau Talata da akwai shugaban hukumar Nukiliya ta Iran Ali Akbar Salihi.
342/